Fatwa
Islamic legal opinions and answers to your questions
assalamualaikum mlm stakanin yin salatin annabi da istigfari wanne yafi falala
Wa alaikum slm, ko wanne yana da falala kuma ko wanne ana buƙatar musulmi yayi. Salatin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama duk wanda yayi ɗaya Allah zai yi masa goma, ana so kafin mutum yayi addu'a ya karanta. Istigfari neman gafara ne a wajen Allah, sannan in mutum yana yi sai samu biyan buƙata duniya da lahira.
As salamu Alaikum mln dan Allah ina da tambaya. Me nene mafi yawan kwanakin yin sallah kasaru
Wa alaikum slm, akwai saɓanin malamai akan wannan mas'alar, wasu suna ganin cewa daga kwana uku za'a bar yin ƙasaru, wasu kuma sun ce ba adadi har sai mutum ya dawo.
As salamu Alaikum Malam ina da tambaya. Mene halaccin yin A,uziyya da Bismillah idan zeyi ikama.
Be halatta ba
assalamu alaikum Mallam nine mahaifiyata Allah yayimata rassuwa sai yakasance danida babana kawai ke gadonta kasan cewar bani da yannai ko kannai sai babana yace ya yafemin nashi rabon Amma Yana da wasu ya'yan daban shin ko yahalatta??? nagode Mallam Allah ya sakamaka da alheri
Wa alaikum slm, idan sauran ƴaƴan ba mahaifiyar ku ɗaya bane dama basu da gadon ta. Ya halatta ya yafe maka rabon sa idan ku biyu kawai zaku ci gadon ta. Koda akwai sauran magadan, idan aka raba zai iya yafe maka
Assalamu alaikum wa rahmatullah Wa barakatuh Malam tambaya ta anan shine menene hukuncin sallah kasaru a kan tafiya shin an kiyasta adadin kwanaki a shari'a wanda idan mutum yayi kasan ya sauka ta kanshi?
Wa alaikum slm, akwai saɓanin malamai akan wannan mas'alar, wasu suna ganin ba iyakar kwanaki, wasu kuma kaman Mazhabar Malikiyya suna ganin cewa iya kwana uku ne kawai za'a yi ana ƙasaru.
Assalamu Alaikum warahmatullahi wabaraka tuh ya sheakh idan akahade sallah magariba da isha'i shin mutun Yana iyayin nafila ko bari zaiyi sai lokacin Isha yayi sannan yayi nafilar Allahu a'alam
Wa alaikum slm warahmatullah, zaka baki sai lokacin Isha yayi kayi Witri
Assalam Alaikum. Don Allah Me Ne Hukuncin Sana'ar (Kwalliya) Ta Mata Ko Kuma (Make Up) A Musulinci? Allah Ƙarawa Malam Lafiya Da Imani.
Wa alaikum slm, ya halatta matukar an kiyaye abinda Shari'a ta iyakance. idan mace ce zatayi wa ƴan uwanta mata kuma ba cakuduwan maza da mata a wajen, ba laifi
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh, I would appreciate the guidance of the scholars and knowledgeable members in this group regarding the following matter. I have accounts with two different banks. With Bank A, when I keep or save money in the account for a period of time, certain charges are deducted, which reduces the amount of money I have. With Bank B, however, when I keep money in the account, the bank adds a certain percentage or amount to my savings over time. My intention is simply to keep my money safe without it being increased or reduced. I do not want to benefit from any additional amount added by the bank, nor do I want my savings to decrease through unnecessary charges. One solution I have considered is keeping my money with Bank B and, whenever the bank adds any amount to my account, giving out the exact amount added. However, I am unsure whether this is the correct approach. I would therefore sincerely appreciate guidance from the scholars on the best way to handle this matter according to Islamic teachings. Thank you, and I look forward to benefiting from your advice. Jazakumullahu Khairan.
Wa alaikum slm warahmatullah, ideally, saving account shouldn't suppose to attract deductions nor any additions. Is just like you keeping your money with someone, and he added some amount or reduced. In our conventional Banking system, which is unislamic, that's normal. But Islamically is not. If you have any access to an Islamic Bank, I advised you go for it, otherwise you better go for current account. Choosing Bank B is not the best solution.
assalamualaikum malam Mae hukunci tsintuwa na naira #1200 Amma na Yi amfani da shi bayan nayi cikiya ban samu Mae shi kuma inda aka Yi tsintuar wajen da mutane ke hada hada ne ne
Wa alaikum slm, idan mutum ya tsinci abinda ya kai ƙimar ayi cikinta, sai ya shekara guda yana cikiya. idan kayi amfani dashi, sai kaci gaba da cikiya, idan aka samu me shi sai ka bashi, idan ba'a samu ba sai ka kayi masa sadaqa dashi
assalamu alaikum Mallam shin ko yahalatta mutum yayi sallah yayi karatun alqur,Ani da azumi domin nemama mahaifiyata Lada idan koma Bai halatta ba Yaya kamata inyi domin nemama Lada da ko gafara nagode Mallam Allah ya sakamako da alheri
Wa alaikum slm, wasu malamai suna ganin ya halatta kayi ibada na nafila domin ladan ya kai wa iyalinsa. Wasu kuma suna ganin sai dai sadaqa, sabo da haka zaka iya yin aikin alkhairi musamman sadaqa, ciyarwa da sauran su
Slm dafatan Mlm Yana lfy Allah yasa haka ameen Tambayata itace Naji malamai sunacewa photo haramune Amma abinda banganeba shine Har photon da akeyi a waya Shima haramunne Ko kokuwa Allah yabada Ikon amsawa chikin sauki
Wa alaikum slm, saɓanin malamai ne akan mas'alar hoto, wasu sun ce hadda na Camera, wasu kuma suka ce wanda aka zana ne Haram. Wallahu Ta'ala A'alam
assalamu alaikum brk ddre yaaiki yamalam inada tambaya ne ,Akan mutum be yayi was Allah alkawari Akan zaiyi azumi 30 Idan yabiyamasa bukatarsa to Kuma akwai ranakun DA baazumi Na nafila acikinsu Toh mutum Zai Iya Yin wnn azumin wata gudadin Ko Kuma de, Allah yakarawa MLM albarka DA ilimi
wa alkm slm, idan yayi alƙawarin jera su dole zai yi, idan kuma yayi 30 be ce a jere ba, to sai ya ajiye bayan kwanakin da ba'a yin azumi yaci gaba