Question
menene hukuncin auren matan da tabar mijinta tsawon shekara bakwai ba da izininsa ba?
Asked by: Muhammad Idris
Answer
Answered by: Dr. Muhammad Abubakar AdamAlhamdulillah Wahdah, Wassalatu Wassalamu ala Rasulil-Lah, wa'ala Ālihi wasahbihi waman Wālāh. bayan haka. Amsa: Wacce tabar gidan mijinta koda na minti daya ne ba da izinin shi ba tayi babban laifi, bare kuma wacce tayi hakan na tsawon shekaru, Lallai babban laifin data aikata yaninninka na wacce tayi haka na ɗan lokaci, kuma Auren mijinta yana kanta har yanzu, matuqar ba shi ne yasaketa ba. Wajibi akanta shine ta tuba zuwa ga Allah, sannan ta nemi gafaran mijintan, Sannan ta koma gareshi ko kuma ta tafi kotu Alkali yaduba matsalar su; yayanke musu Hukunci na ci gaban zamansu ko sabanin shi. Wasallahu Wasallama ala nabiyyina Muhammadin wa'alihi wasahbihi ajma'een.
Answered on May 16, 2026
Related Fatwa
Mallam Ni mutum ne me yawan aikata istiminai,pls abani shawara
kaji tsoron Allah ka kuma guji duk abinda zai kai ka zuwa ga aikata wannan laifin kaman kallon video ko hotuna da basu dace ba. sai kuma ka yawaita a...
Read Full Answer →dan Allah ina tanbaya malam mai nene aki dar yan shi a kuwa
Alhamdulillah Wahdah, Wassalatu Wassalamu ala Rasulil-Lah, wa'ala Ālihi wasahbihi waman Wālāh. bayan haka. Amsa: Aƙidar yan shi'a itace a dunƙule k...
Read Full Answer →Assalamu alaikum warahmatullah malam Dan Allah ya halarta mace tayi sallah da niqaf a fuskarta
Wa'alaikussalamu Warahmatullah Wabarakatuh. Amsa: Ya halatta tayi hakan, musamman idan akwai namiji wanda ba Muharraminta ba a gurin. Allah yai ma...
Read Full Answer →Assalamu Alaikum warahmatullahi wabaraka (Kalmar Bari بارى) tana cikin sunayen Allah? Idan za'akora...
Wa'alaikussalamu Warahmatullah Wabarakatuh. Amsa: Eh, hakane, Abdul-Bari za'a ke kiran shi, kamar dai sauran Masu sunayen irin hakan; Abdullah, Abdu...
Read Full Answer →Aslm malam. Don Allah ya ake hudubar sawa yaro suna? nagode
Wa'alaikussalamu Warahmatullah Wabarakatuh. Amsa: Babu Wata huduba da aka shar'anta domin sanya wa yaro suna a musulunci. wajibi shine zaba mai suna...
Read Full Answer →malan ni mutum ne me yawan kokanto da raye raye na zuciya haka yasa kome nayi senaringajin riya n...
Sai ka din ga addu,ah Allah ya yaye maka
Read Full Answer →